letras.top
a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 #

letra de har abada - hamisu breaker

Loading...

har abada ina yabawa masoyiya
tunda ta shigeni raina ta kewaya
halayyarta ba misali mai kyan niyya
irin nata ban gani ba

kullum ke nake gani a idona
kalamanki sun shige min raina
kinji amona sahiba! kizo da kauna
ke zan lallaɓa muradi na raina
shin ya za’ai inada ke
kamar atafa kike a hasken haƙora
wane madara idonki kece na wara
ko kinyi fushi kinada kyau, balle harara
ni wannan za na mallake

wata alfarma nake biɗa! yanzu yanzu
ba sai anjima ba zai zamma dazu
kiyi na’am kawai dani, so ya wanzu
burina a bani ke

lallai so yanada daɗi da gaske
amma in ka samu mai ji da gaske
mai alƙawari tayo cikashi yanke take
bana son nisa da ke

ko kince in dakata ban tsayawa
sonki yanata zabura ni ban iyawa
da kin barni na sani ban hayewa
ta ya za na tsallake

ƙwarin gwiwa, sarewa, duka duk yana ga ke
ko bacci nake da na tuna ke sai in wartsake
in zaki taimaken ki ban dama in zama dake
dan na gasgata samun nutsuwa dole sai dake

letras aleatórias

MAIS ACESSADOS

Loading...